WASHINGTON, DC —
Shugaba Barack Obama na Amurka da magoya bayansa sun mike wajen caccakar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, Mitt Romney, bisa fatan samun madafar da zata ingiza su gaba kafin Babban Taron Tsayar da Dan Takara na Jam'iyyar Democrat da za a fara cikin wannan makon.
A lokacin da ya yada zango domin yakin neman zabe a Jihar Colorado, Mr. Obama ya soki manufofin tattalin arziki na Mr. Romney, yana mai fadin cewa, "kasar nan ta kai gaccin da bai kamata a maida mata hannun agogo baya ba." A lokacin da jama'a suka mike su na kushe 'yan Republican, sai shugaban ya ce, "ba kushe su zaku yi, ku fito ku jefa kuri'a."
Mr. Romney ya shafe safiyar jiya lahadi a cocinsa dake Wolfeboro a Jihar New hampshire. Amma wani babban mashawarcinsa, Eric Fehrnstrom, ya yi watsi da wannan suka yana mai fadin cewa akidar Mr. Romney ta samar da karin ayyukan yi da kyautata albashi, ta sha bambam da abinda ya kira "gazawar shugabancin Obama."
Kuri'ar neman ra'ayoyin Amurkawan da suka yi rajistar jefa kuri'a wadda Reuters/Ipsos ta gudanar ta nuna cewa Mr. Obama da Mr. Romney duk su na da goyon bayan kashi 45 cikin 100.