WASHINGTON, D.C - Amma rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta gudanar da bincike ba saboda rahoton ba gaskiya ba ne.
Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) wacce gwamnati ta nada, a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na yanar gizo ranar Talata, ta ce za ta kaddamar da kwamitin na musamman a mako mai zuwa a Abuja.
"Hukumar kare hakkin bil'adama ta kasa za ta kaddamar a ranar Talata 7 ga Fabrairu 2023, da kwamitin bincike na musamman kan take hakkin dan Adam wajen aiwatar da ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso gabas," in ji NHRC.
“Kwamitin zai mayar da hankali ne kan binciken rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters wanda ya yi zargin cewa sojojin Najeriya na da hannu wajen zubar da ciki da dama a yankin Arewa maso Gabas a cikin shekaru 10 da suka wuce,” in ji NHRC.
Kwamitin mai mutane bakwai zai kasance karkashin jagorancin alkalin kotun koli mai ritaya Abdu Aboki kuma ya hada da Manjo Janar mai ritaya da wakili daga kungiyar lauyoyin Najeriya da kuma kwararre a fannin kula da lafiyar mata masu juna biyu da mata, in ji NHRC.
Kawo yanzu dai ba a bayyana tsawon lokacin da binciken zai dauka da kuma abin da kwamitin zai yi da sakamakon binciken ba. NHCR ba ta da ikon gurfanar da masu take haƙƙin ɗan adam, amma tana iya ba da shawarar gurfanar da masu laifi.
-Reuters