A jiya Lahadi masu zanga-zanga a Iran sun fantsama akan titunan birnin Tehran, da kuma wasu sauran garuruwa, kwanaki biyu a jere kenan, bayan da gwamnatin Iran ta fadi cewa, ita ta harbo jirgin saman fasinjan kasar Ukraine, ranar Larabar da ta gabata, wanda yayi sanadiyar halaka mutune 176 da ke cikin jirgin.
Tun da farko dai gwamantin Iran ta kafe akan cewa zargin harba makami mai linzami farfagandar kasashen yammacin duniya ne kawai.
Yanzu haka gwamantin Iran tana ci gaba da fuskantar matsin lamba daga cikin gida da kasashen ketare.
Amma har yanzu babu wata alama da ta nuna cewa zanga-zangar za ta jirkice ta zama ta kin jinin gwamnati.
A ranar Asabar din da ta gabata ne aka fara gudanar da zanga-zangar, yayin da masu zaman makoki a Tehran suka bayyana fushinsu ga shugabannin Iran.
Masu boren sun sake fitowa a jiya Lahadi a matsayin amsa wani kira na ma'abota kafafen sadarwa na zamani, da karfi suna fadin cewa jagoran addinin kasar "ya yi murabus, da kuma fatan mutuwa akan makaryata."
An kuma tura ‘yan sandan kwantar da tarzoma wuraren dan-dazon jama’a a duk fadin babban birnin kasar.
Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani, wadanda Muryar Amura ba ta tantance su ba, sun nuna yadda zanga-zangar ta watsu zuwa garuruwan Isfahan da Rasht.
Facebook Forum