Koda yaushe akan ba da sanarwa shugaba Muhammad Buhari ya yi magana da wani ko wasu ta wayar tarho ba tare da jin muryarsa ba.
Wani tsohon minista Alhaji Umaru Dembo kuma magoyin bayan Shugaba Muhammad Buhari ya yi tsokaci akan irin halin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki.
"Duk da cewa shugaban ya mika mulki kafin ya tafi hutu da neman jinya kullum ana cewa ya gaisa da wani ko ya kira wancan saboda shi dan Najeriya muddun aka ce wanda yake so yana nan lafiya to bai damu da wani abu ba." In ji Dembo.
Dangane da zargin da ake cewa 'yan baranda sun mamaye gwamnatin Buhari, Alhaji Dembo ya ce ba za'a yi musu ba akan dabarun 'yan Najeriya inda ya ce ko a lokacin 'Yar'adu'a da ya samu rashin lafiya haka aka dinga yi ana rudar mutane.
Ya ce saboda haka mutane na iya yin komi saboda son ransu domin sau tari mutane ba su damu da yadda mulki ke tafiya ba amma sun damu da abubuwan da suke so da kuma moriyar da za su ci.
Sai dai mai baiwa shugaba shawara kan harkar yada labarai, Femi Adesina, ya sa suna ba da rahoto akan shugaban ba kamar yadda ake masu zargin suna boye bayanai a kansa ba.
Domin jin cikakken rahoton saurari rahoton wakilinmu Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum