Dalibai da dama na Jami'ar George Washington suka halarci taron domin fahimtar mahimmancin aikin jarida daga kwararru da suka hada da tsohon shugaban Muryar Amurka kuma daraktan aikin jarida da tsaron kasa na Jami'ar David Ensor, da Aliyu Mustaphan Sokoto babban editan Sashen Hausa na Muryar Amurka da kuma Euna Lee mai shirya tsare-tsaren talibijan na sashen Koriya na Muryar Amurka.
Ranar 2 ga wannan watan Afirilu aka yi zaman.
Tsohon daraktan Muryar Amurka David Ensor ya fara da cewa yayinda muka zamanto masu fadin gaskiya game da kasarmu muke kuma bayar da labari akan kasarmu koda bashi da dadin ji kamar labarin fafutikar kungiyar rajin kare bakaken fata ta Black Lives Matter da yadda 'yan sanda kan kashe bakaken fata da dai sauran batutuwa. David ya ce "gaskiya akwai tabargaza a kasarmu. Akwai abubuwa da dama a kasarmu da ko muma basu birgemu ba"
David ya ci gaba da cewa idan ka fadi gaskiya sai masu saurarenka su dada yawa saboda sun yadda da kai bisa fadin gaskiya game da kasarka da matsalarta. Wasu ma sai su saurareka idan ka yi magana akan kasarsu.
Ita ma Euna Lee ta sashen Koriya a Muryar Amurka wadda aikin jarida ya yi sanadiyar zamanta a kurkuku har na kwanaki 140 a Koriya ta Arewa bisa zargin ta tsallaka iyakar kasar ba tare da izini ba, ta ce suna shirin kirkiro da shirye-shirye guda bakwai har da wani na kowane mako na tsawon mintuna 20 inda kwararru zasu shigo su yi fashin baki akan abubuwan dake faruwa a Koriya ta Arewa. Ta kara da cewa mutanen Koriya ta Arewa na marmarin jin labaran duniya.
Shiko babban editan sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustaphan Sokoto ya yi jawabi ne akan mahimmancin dan jarida ya iya harsuna daban daban. "Abun da zan ce akan koyon harsuna da alakarsu da aikin jarida a duniyar nan shi ne duk wata kasa tana jin akalla yare uku na makwafciyarta kamar a yammacin Afirka inda ana tafiya da fasfo daya wanda ya taimaka wajen harkokin kasuwanci. Lallai duk dan jaridan da yake jin harsuna da yawa zai yi aikinsa cikin sauki koina yake". Ya ce kowa a Muryar Amurka yana jin akalla yare uku. Ya ce shi kansa yana jin yare har da na Sabea domin ya yi karatu a can.
A karshe daliban sun yi tambayoyi da dama akan ayyukan jarida.
Ga Abdoulaziz Adili Toro da karin bayani a wannan rahoton.
Facebook Forum