Da misalin hantsi ne aka yi jana'izar a makarbartar unguwar Sagata a birnin Yamai inda aka binne daliban makarantar firamarin Pays Bas wadanda suka rasu sakamakon wannan gobara.
Domin karrama wadanan yara an yiwa gawawwakinsu likkafani da turar Jamhuriyar Nijar.
Daruruwan mazaunan birnin Yamai da suka hada da iyaye da dangi da abokan zama ne suka fito don yi wa wadannan dalibai rakiya zuwa makwancinsu na karshe.
Kwanaki 3 bayan faruwar wannan mummunan al’amari, har yanzu wani mutun mai suna Boubacar Souley na tunawa da yadda ya tarar da gawar jikarsa kwance cikin burbushin wuta.
Bayan kammala aiyukan bizne wadanan dalibai an nufi makarantar da abin ya faru inda aka taru don yin addu’oi.
Karin bayani akan: Mohamed Bazoum, daliban, Nijar, da Nijer.
Kakakin gwamnati Minista Tidjani Abdouldari da ke daya daga cikin ministocin da shugaba Mohamed Bazoum ya aika a wurin wannan zama, ya ce gwamnati za ta tallafawa iyayen yaran da suka rasu a wannan gobara.
Sakataren kungiyar malaman makaranta ta SNEN Issouhou Arzika, ya sake jaddadawa hukumomi bukatar daukan matakan kiyaye sake aukuwar irin wannan tashin hankali.
A yammacin Talatar 13 ga watan Afrilu da ta gabata ne gobara ta tashi a makarantar fraimarin Pays Bas inda dakunan karatu na zana kimanin 27 suka kone kurmus lamarin da ya yi sanadin mutuwar dalibai galibinsu ‘yan kasa da shekaru 5 da haifuwa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: