Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kashe Dalibai 20 A Wata Makarantar Firamarin Yamai


Daliban Firamare 20 Sun Mutu a Gobarar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:34 0:00

Daliban Firamare 20 Sun Mutu a Gobarar Nijar

Gobarar da ta tashi a wata makarantar firamarin birnin Yamai ta haddasa rasuwar dalibai da dama yayin da baki dayan dakunun karatu suka kone kurmus.

Lamarin ya sa hukumomin ilimi a matakin jihar suka rufe makarantu a tsawon wunin laraba 14 ga watan maris domin nuna juyayin faruwar wannan al’amari da har yanzu ba a san tushensa ba.

Lamarin ya faru ne bayan karfe 4 na la’asariyar talata a dai dai lokacin da daruruwan dalibai ke daukar karatu a wata makarantar frimarin n’guwar Pays Bas mai dakunan karatu kusan 30 dukkansu na zana.

Fira minister Ouhoumoudou Mahamadou tare da maya bayan ministan ilimi Dr Rabiou Ousman da na cikin gida Alkache Alhada da gwamnan yamai Oudou Ambouka sun ziyarci makarantar da wannan mumunan iftila’I ya afkawa jim kadan bayan jami’an kwana kwana sun kashe wannan gobara.

Karin bayani akan: Mohamed Bazoum, daliban, Nijar, da Nijer.

Fira ministan ya ce "mun zo ne don mu jajantawa jama’a faruwar wannan abin bakin ciki domin yaran da abin ya rutsa da su ‘yayanmu mu duka kuma zamu gudanar da bincike domin gano tushen wannan gobara".

Karantar da yara a dakunan karatun da aka yi su da darni ko zana wata dadaddiyar matsala ce da dalibai da malaman makaranta suka sha korafi akanta saboda la’akari da hadarin da take tattare da shi. Sabon shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum a jawabinsa na rantsuwar kama aiki ya sha alwashin dakatar da karantarwa a irin wannan dakuna da ake kira classe paillote a faransance.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Yadda Na Samu Labarin Gobarar Da Ta Yi Sanadin Mutuwar 'Yata

Yadda Na Samu Labarin Gobarar Da Ta Yi Sanadin Mutuwar 'Yata
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00

Wani mahaifi da 'yarsa ta rasu a gobarar da ta kashe yara dalibai 20 a makarantar firamare a Nijar, ya fadi yadda ya samu labarin tashin gobarar inda ya ce, kafin ya isa wurin, wutar ta riga ta lakume ajujuwan da daliban suke.

XS
SM
MD
LG