Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta Transparency International tare da tallafin kungiyar hadin gwiwar OXFAM a karkashin kungiyar DANIDA ta fara wani taro na ba matasan kungiyar AJIDEN horo akan yadda zasu fadakar da al'umma game da illar cin hanci da rashawa a cikin harkokin tafiyar kasa.
Wannan na zuwa ne bayan wani bincike da Kungiyar ta Transparency International ta fitar wanda ta ke fiddawa a ko wace shekara dangane da ci gaban al’umma da kuma tattalin arziki.
Sakataran watsa labarai na kungiyar Transparency International reshen Jamhuriyar Nijar, Malam Sharif Issoufou, ya ce suna bai wa matasan horo ne a wurare dabam-daban a wasu garuruwa domin su san yadda za su rinka gudanar da aikin su musamman kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma abinda doka ta shimfida.
A nahiyar Afrika, a wasu lokuta jami'an tsaro sukan wuce gona da iri wajan rike mutum a offishin su fiye da lokacin da doka ta tanadar saboda jama'a da dama na jahiltar ‘yanci da hakkokinsu ko da jami'an tsaro suna tuhumar su da wani laifi, shi ya sa kungiyar ta Transparency ke son ta hanyar matasan ta wayar da kan al'umma domin su san kan dokoki da hakkokinsu.
Wannan horon na zuwa ne a daidai lokacin da cin hanci da rashawa ke neman wuce gona da iri da kuma yadda jami'an tsaro a wasu kasasshen nahiyar Afrika ke ci gaba da turnike yunkurin ci gaban nahiyar a fannin tattalin arziki da ma ci gaban rayuwar al'umma.
Saurari cikakken rahoton Haruna Mamane Bako:
Facebook Forum