Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Soki Matakin Burundi Na Dakatar Da Ayyukan Kungiyoyi Masu Zaman Kansu a Kasar


Yan Gudun Hijirar Burundi
Yan Gudun Hijirar Burundi

Kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa sun koka kan matakin da gwamnatin kasar Burundi ta dauka na dakatar da aiyukan kungiyoyi masu zman kansu, duk kuwa da damuwar da ake ita ta cin zarafin bil Adama a kasar.

Matakin da majalisar tsaron kasar ta dauka na dakatar da duk wasu ayyukan kungiyoyin, ya shafi kungiyoyi kamar kungiyar likitoci ta "Doctors Without Borders" da kungiyar kiristocin katolika ta "Catholic Relief Services", wadanda ke bayar da taimakon kiwon lafiya a wasu kasashen da mutanensu ke matukar bukata.

Nicolas Agostini na wata kungiyar bada agaji ta MDD dake kare marasa karfi, yace wadanan kungiyoyin da aka dakatar sune ke aikin samarda aiyukkan kiyon lafiya da na ilmi da gwamnatin Burundi din bata samarwa.

Tun shekarar 2015 kasar Burundi ke fama da tashe-tashen hankalin siyasa. bayanda shugaban kasa Pirre Nkurunziza, ya sanar da kudurinsa na sake tsayawa takara a wa’adi na uku, ya kuma yi watsi da sukar da ake masa na cewa wa’adi biyu ne kawai kundin tsarin mulki ya bashi damar yi. Tun daga lokacin ne jami’an tsaro da matasan jam’iyya mai mulki, ke auna ‘yan adawa da kame da fyade da kuma azabtarwa harma da kashe su, a cewar kungiyar kungiyar kare ‘yancin dan adam ta Human Rights Watch.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG