An gudanar da taron kwamitin CNDP a dakin taro na « salle des banquets » dake fadar Frai Minista Briji Rafini da wakilan jam’iyyun siyasa.
Wannan kwamitin shi ne yake da alhakin warware rigingimun siyasa. Taron ya zo ne da bukatar nazari akan maganar gyaran fuskar kundin tsarin zaben da a can baya ya haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin jam’iyyun siyasa.
Bayan da aka saurari shawarwari daga wakilan jam’iyyun siyasar da suka halarci wannan taro a karshe an yanke shawarar kafa kwamiti mai mambobi 12 wadanda za su duba hanyoyin yiwa wannan kundin tsarin zabe gyaran fuska kamar yadda shugaban jam’iyyar PNDS TARAYYA kuma ministan cikin gida BAZOUM MOHAMED ya gayawa manema labarai. Ya ce an bukaci ‘yan adawa su kawo mutane 8, su kuma su kawo mutum 4. Yace duk da adawar da ake yi masu sun amince da hakan. Ya kara da cewa duk abun da ‘yan adawa suka kawo idan ya dace za su amince dashi, da fatan su ma za su yadda da nasu shawarwarin.
Jam’iyar MPN KISHIN wace rashin yarda da wannan kundin tsarin zabe ya yi sanadiyar ficewar ta daga kawancen jam’iyyu masu mulkin Nijer ta halarci wannan taro. Mataimakin shugabanta KORONE MASANI yace dama ce a garesu su kara fahimtar da wadanda ba su gane manufar jam’iyar ba. Ya ce tun farko su ne suka fara dagewa sai an yi gyara. Sun kwashe wata 11 suna adawa akai saboda haka garesu faduwa ce ta zo daidai da zama.
Sai dai a yayinda ake gudanar da wannan taro shuwagabanin kawancen jam’iyyun adawa na FRDDR ana su bangare sun kira taron manema labarai domin sanarda jama’a dalilansu na kauracewa wannan taro na CNDP .
MAMAN SANI ADAMOU shine kakakin jma’iyun hamayya. Yace babu yadda za’a ce a zo a zauna ba tare da canza dokoki ba. Sai an yi hakan kana su ma su shiga taron duk wani gyare gyare da za’a yi. Dole ne a fara da abun dake hana ruwa gudu.
Rashin yarda da dokokin dake kunshe cikin kundin tsarin zaben kasar ta Nijer ya ja wa hukumar zabe ta CENI bakin jini daga wajen ‘yan adawa saboda haramtatta ce dalili kenan da suka ki aikewa da wakilai a wannan hukuma mai mambobi 13 yayinda shirye shiryen zabeN 2021 ke kara kankama.
A saurari rahoton Souley Barma
Facebook Forum