Magamar hanyar « premier echangeur » dake kan titin da ake kira AVENUE MALI BERO, ta kasance daya daga cikin wuraren da aka fi huskantar cinkoson ababen hawa a Yamai.
A wannan safiya ta litinin 1 ga watan Oktoba, kusan galibin matuka sun daura madaurin da ake kira ceinture de securite ko (seat belt) da turancion ingila, yayinda akan ganin mafi yawancin masu babura sanye da hular kwano da nufin yin biyayya ga dokar da hukumomi suka kafa. Wani matukin babur Malam Chaibou Aboubakar na ganin fa’idar wannan mataki. Ya ce kwanakin baya ya fadi sai da ya yi juyi hudu kafin ya samu kansa. A wancan lokacin idan da bai sa hular ba da an manta dashi yau.
Haka su ma masu motoci ke yabawa da wannan tsari koda yake suna ganin a cewarsu abin na bukatar gyara. Amma sun kira a yi biyayya da dokar.
Tuni dokar ta fara rutsawa da wasu masu ababen hawa irinsu Iliyasu wanda ‘yan sanda suka kwace wa inji da hantsi, saboda samunsa da rashin saka hular kwano. Ya ce da ya san haka ne da bai fita da abun hawa ba, sai ya ajiye gida har sai ya samu kudin sayen hular.
A ranar 10 ga watan jiya ne hukumomi suka sanarda jama’a cewa saka hular kwano da amfani da madaurin mota (seat-belt) wajibi ne ga jama’a daga ranar 1 ga watan Oktoba abinda shugaban kungiyar direbobin taxi Batada Jibril ke cewa ba su gamsu da shi ba. Acewarsa irin wannan dokar ana ba mutane wa’adin watannin shida ko uku kafin ta fara aiki ba a yita farat daya ba.
Domin kawarda dukkan wani shakku daga zukatun jama’a, wani jami’in kula da zirga zirga da muka tarar yana bada hannu ya ce kowa ya kwantar da hankalinsa yana cewa doka doka ce. Kowa ya shirya binta saboda mutane su tafi lafiya su dawo lafiya. Ya ce dokar ba ta nufin takurawa kowa
Doka tace dukkan wanda aka kama da laifin kin amfani da hular kwano ko madaurin mota za a ci shi tara daga 5000 zuwa 10000 tasefa, cfa.
A saurari rahoton Souley Barma
Facebook Forum