A wani jawani da ya yi wa al'ummar jihar, gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana wa al'ummar jihar cewa an samu bullar kwayar cutar a jihar, bayan da aka gano wani wanda bai dade da dawowa daga jihar Kano ba ya kamu da kwayar cutar.
Mr. Solomon Kumangar, daraktan yada labaran gwamnatin jihar ya yi karin haske game da jawabin gwamnan da kuma matakan da gwamnatin jihar ta dauka a yanzu da suka hada da killace wanda aka tabbatar yana dauke da cutar, sannan ya ce akwai mutane 55 da aka tabbatar mutumin yayi mu’amalla da su bayan dawowar sa, suma yanzu ana kokarin yi musu gwaji domin a tabbatar da lafiyar su.
Mr. Solomon Kumangar ya kara da cewa, gwamnatin jihar zata kafa dokar hana fita kamar yadda aka kafa a wasu jihohin.
Kamar jihar Adamawa, ita ma jihar Taraba tuni ta kafa dokar hana zirga-zirga. Masarautar Muri ta fitar da wata sanarwa ta hannun sakataren masarautar Alhaji Umar Sa’ad Gassol, tana jaddada sanarwar mai alfarma Sarkin Musulmi akan matakin dakatar da Tafsir da kuma sallolin Tarawih da Tahajjud kamar yadda aka saba a watan azumi.
Sanarwar ta kuma bukaci kada jama'a su yi kunnen kashi da matakin domin kauce wa yada cutar.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum