Kafafen yada labarai sun yi ta ba da rahotanni kan yadda dan wasan Atletico Madrid Luis Suarez ya barke da kuka bayan da kungiyarsa ta lashe kofin gasar La Liga na bana a ranar Asabar.
Atletico ta doke Real Valladolid a wasan karshe na gasar La Liga da ci 2-1, wanda a karshe ya ba damar lashe kofin- ko da yake, an hangi ita za ta lashe kofin.
Angel Correa da Suarez ne suka zura wa Atletico kwallayenta bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.
A tashin farko Valladolid ta zura kwallonta ta hannun dan wasanta Oscar Plano tun kafin a je hutun rabin lokaci.
Masu sharhi a fannin kwallon kafa da masoya wasan, sun yi ta tsokaci kan abin da ya sa Suarez kuka.
Ko da yake, ba bakon abu ba ne dan wasa ya yi kuka bayan samun nasara, domin akan fassara hakan a matsayin kukan-dadi – wanda ittifakin masu sharhi ya nuna cewa ba shi ya sa Suarez kuka ba.
“Barcelona ba su nuna ina da daraja ba amma Atletico sun karbe ni hannu-bi-biyu. Zan kasance mai ci gaba da gode wa kulob din da suka yi na’am da ni.” Suarez ya fada yayin hirar da aka yi da shi a talabijin kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito.
Suarez ya fashe da kuka a lokacin da alkalin wasan ya hura wusur din karshe, inda ya zauna a kasa yana hawaye yayin da aka gan shi rike da waya yana magana da iyalansa da abokanai ta manhajar Facetime.
Daga Barcelona Suarez ya koma Atletico, wacce ake ganin ta masa kora da hali, inda Atletico ta karbe shi akan kwantiragin shekara biyu.
An dai ya ta samun sabanin tsakanin Suarez da Barcelona a lokacin yana kulob din, lamarin da ya kai ga har ana ajiye shi a gefe a wasanni.
Takaddamar ta kai ga Lionel Messi ya barazanar barin Barcelona dalilin wannan rashin jituwa.
Wannan shi ne karon farko cikin shekara bakwai da Atletico ta ci kofin gasar.