Shugabannin juyin mulkin sun fitar da sanarwa yau jumma’a cewa, sun saki Kafando da ministoci biyu da suke tsare da su, domin a zauna lafiya.
Basu yi karin haske a kan Firai Minista Isaac Zida wanda suka kama tare da shugabana kasar ranar Laraba ba.
Birgediya janar Gilbert Diendere, shugaban sabuwar majalisar gudanarwar kasar yayi hira da sashen Faransanci na Muryar Amurka jiya alhamis kwana daya bayanda sojoji suka hambare gwamnatin rikon kwaryar kasar suka kama shugabananinta.
Janar din yace sun yi juyin mulkin ne sabili da akwai alamar tambayar a tsarin siyasar kasar. Yace zai fara tattaunawa da dukan bangarorin siyasa.
Dama anyi shirin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa ranar 11 ga watan Oktoba. Sai dai yanzu babu tabbacin ko za a kiyaye ranar.
Jiya alhamis Fadar white House tayi allawadai da kwace mulkin, ta kuma yi kira da a saki shugaban kasar da Firai ministan ba tare da bata lokaci ba.