Janar Gilbert Diendere wanda ya kasance shugaban juyin mulki a kasar Burkina Faso kuma shugaban majalisar sojoji dake rike da madafin iko ya ce tsohon shugaban kasar da Firayim Ministan suna nan tsare a barikin soji kuma nan ba dadewa ba za'a sakosu.
Janar Diendere ya shaidawa Muryar Amurka sashen Faransanci haka ne jiya Alhamis kwana daya bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin wucin gadi ta kasar Burkina Faso dake yammacin Afirka kana suka tsare shugaban kasa da firayim ministansa.
Shugaban mulkin sojan yace sun hambarar da gwamnatin ne saboda bangaranci da ya mamaye harkokin siyasar kasar. Yace zai soma tattaunawa a siyasance da duk jam'iyyun siyasa dake kasar.
Kafin wannan juyin mulkin da ya auku ba zato ba tsammani an shirya gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa ranar 11 ga watan Oktoba. Bisa ga duk alamu shirin ya sha ruwa yanzu.
Yayinda sojoji suka mamaye fadar gwamnatin kasar dake birnin Ouagadougou matasa sun yi ca sun soma zanga zangar kin juyin mulkin lamarin da ya haddasa mutuwar akalla mutane uku.
Kazalika ofishin jakadancin Amurka yace sojoji sun kafa shingaye a duk titunan birnin.
To ko gwamnatin zata iya tsayawa da kafafunta? Sai a sa ido a gani saboda gwamnatin Amurka ta yi watsi da juyin mulkin tana cewa ba za'a amince da kwace mulki ba ta bayan gida. Ta kira sojojin su mayar da gwamnatin da suka hambare.
Haka ma mataimakin shugaban kungiyar kasashen Afirka Erastus Mwencha ya bukaci sojojin jiya Alhamis da su yi maza cikin hanzari su mayar da gwamnatin da suka kawar.
Ya kara da cewa duk gwamnatin da ba'a zabeta ba ko kafata kan kundun tsarin mulkin kasa haramtacciya ce saboda "bamu yadda da karya doka da oda ba" inji Mwencha. Yace kowane canjin gwamnati dole ne a yi ta hanyar da ta cancanta.
Idan ba'a manta ba an kafa gwamnatin wucin gadin ne bayan da masu zanga zanga suka tilastawa shugaban kasar na lokacin Blaise Compaore sauka daga shugabancin kasar bayan ya kwashe shekaru 27 yana mulki. Kafin a tayar masa da bori Compaore yana shirin canza kundun tsarin mulkin kasar da nufin kara wa kansa wa'adin mulki.
Abun kulawa dashi nan shi ne Janar Gilbert Diendere wanda ya yi juyin mulkin dadadden abokin Balaise Compaore ne na kud da kud. Ya ma yi korafin cewa gwamnatin wucin gadin ta hana magoya bayan Compaore tsayawa takara ko neman kowane mukamin siyasa.