Lauyan dake kare tsohon shugaban Junhuriyar Nijer Mamadou Tandja yace wata kotun daukaka kara tayi watsi da duk zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi mishi, kuma ta bada umurnin a sake shi daga tsarewar da ake mishi a gidan wakafi.
A yau ne lauyan , Souley Oumarou yake gayawa manema labarai a birnin Yamai cewa nan bada dadewa ba za’a saki tsohon shugaban. A bara ne dai soja suka tumbnuke gwamnatin ta tandja bayanda ya chanja kundin tsarin mulki don yayi ta-zarce da kuma kara wa kansa yawan iko.
Bayan sun tumbuke shi ne sojojin Nijer din suka fito suna zargin cewa daga lokacinda Tandja ya kama mulki a shekarar 1999 zuwa sauke shi, ya sace $dala milyan 125 (na Amurka).
A lokacin mulkin na Tandja, Nijer ta sami dubban milyoyin daloli daga ma’adininta na uranium¸ amma kuma duk da haka kasar taci gaba da zama a sahun gaba na kasashe mafi talauci a duniya.