Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saka Dokar Hana Fita a Kananan Hukumomi Uku A Filato


'Yan sandan Najeriya yayin da suke wani atisaye (Facebook/NPF)
'Yan sandan Najeriya yayin da suke wani atisaye (Facebook/NPF)

“Daukan matakin ya zama dole saboda rahotannin da aka tattara kan tsaro sun nuna cewa akwai barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.”

Gwamnatin jihar Filato ta saka dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Jos ta Kudu da kuma Bassa, bayan kisan da wasu matasa suka yi wa wasu Fulani matafiya a hanyar Rukuba Road da ke kusa da gada Biyu a birnin Jos.

Dokar za ta fara aiki ne daga karfe biyu na ranar Lahadi 15 ga watan Agustan 2021 wacce za ta hana fita baki daya.

Wata sanarwa da Darektan yada labaran gwamnatin jihar ta Filato wacce ke tsakiyar arewacin Najeriya ta ce, an dauki matakin ne don a dakile yiwuwar barkewar tarzomai.

“Daukan matakin ya zama dole saboda rahotannin da aka tattara kan tsaro sun nuna cewa akwai barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.” In ji Darektan yada labarai Dr. Makut Simon Macham.

Gwamnan Filato Simon Lalong (Facebook/PLSG)
Gwamnan Filato Simon Lalong (Facebook/PLSG)

A ranar Asabar wasu matasa suka kashe Fulani matafiya da suka taso daga jihar Bauchi yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kudancin Najeriya.

Wasu rahotanni sun ce adadin Fulanin da aka kashe ya haura 30 yayin da wasu ke nuna cewa bai ka haka ba.

Kazalika wasu rahotanni sun yi nuni da cewa ba a ga wasu mutum 50 ba.

Sai dai wata sanarwa da gwamna Simon Lalong ya fitar a ranar Asabar a shafin sada zumunta ta ce, mutum 23 aka kashe daga cikin matafiyan yayin da 23 suka samu raunuka. Gwamnan ya kara da cewa an kubutar da mutum 26.

Lalong ya ce an kama mutum 20 da ake zargin na da hannu a lamarin.

"Kada a danganta wannan dayen aiki da abin da ya shafi kabilanci da addini." Lalong ya kara da cewa.

Fulanin sun halarci taron bikin sabuwar shekarar addinin Islama da Sheikh Dahiru Bauchi ya gudanar ne a Bauchi, sun kuma yi jerin gwano ne cikin motocin bas kirar Hummer guda biyar don komawa gıda a lokacin da suka gamu da ajalinsu a yankin na Rukuba Road da ke kusa da Gada Biyu.

Wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a daidai lokacin da al'umar Irgiwe ke gudanar da jana'izar wasu mutanensu da aka kashe a wani rikici mai nasaba da kabilanci da ya auku a kwanan nan.

XS
SM
MD
LG