An rantsar da shugaba Goodluck Jonathan a cikakken wa’adinsa na farko akan mulki. A gaban dubban mutane cikin harda wasu shugabanin kasashen Afrika aka rantsar da shugaban na Nigeria a yau lahadi. Babar kalubalan dake gaban shugaba Jonathan shine yadda zai hada kan kasar, wadanda tarzomar bayan zaben da suka kashe fiye da mutane dari takwas ta raba kawunansu. In dai ba’a mance ba a watan mayun bara shugaba Jonathan ya dare kan ragamar mulki bayan rasuwar tsohon shugaba Umar Musa Yar’adua.
A jawabin daya gabatar bayan an rantsar dashi, shugaba yayi alkawarin inganta harkokin illimi da samar da aiyukan yi da kuma gudanar da harkokin raya kasa a illahirin nahiyar Afrika. Shugaba Jonathan ya kuma ce yana wakilta bege da bukatun dukkan yan Nigeria
Yace ayan kwanaki masu zuwa, tilas su wadanda jama’a suka zaba,su nuna cewa su, masu kishi kasa ne, domin biyan bukatu da begen dukkan yan Nigeria. Yace tilas ne kuma su nuna shugabanci na gari da yin aiki tukuru domin canja alkiblar kasar.