Ranar Yara Ta Duniya A Nigeria
A daidai lokacinda ake shagalin Ranar Maida Hankali Kan Yara ta Duniya, dimbin matsalolin dake addabar harakar ilmi a Nigeria suna dada kawo cikas ga burin yaran na neman ilmi mai zurfi da zai kai su ga samun shiga fannonin sana’oi daban-daban a rayuwarsu. Wakilin Muryar Amurka (VOA) na jihar Yola, Ibrahim Abdulaziz ya dubi yadda dogon yajin aikin da malamai suka yi wata da wattani suna yi a jihar Taraba yake ci gaba da takura wannan burin na yara ‘yan makaranta. Ga rahotonsa: