Tuna irin masifar da suka shiga a bara a sanadin ambaliyar ruwa, yasa hankalin mutane da daman a jihohin Sokoto da kebbi yake a tashe saboda tsoron abinda zai faru a bana. Wannan fargabar ta biyo bayan hasashen da aka yi na cewa mai yiyuwa ne a sami ruwan sama a wannan shekara fiyeda da na bara. A shekarar da ta gabata dimbin mutane sun rasa muhallansu da gonnaki a sanadin faccewar madatsar ruwa ta Goronyo wacce itace madatsa ta biyu a girma a duk fadin Afrika, Wakilin Muryar Amurka a Sokoto, Murtala Faruk Sanyinna ya zanta da wasu mazuna karamar hukumar Goronyo da suka ce suna cikin damuwa ganin har yanzu ba’a warware matsalolin da suka janyo ambaliyar bara ba. Ga rahoton:
Fargabar Ambaliya A Jihohin Sokoto Da Kebbi