Yansanda a arewacin Najeriya suna bincike fashe-fashen boma baman da suka auku a wani barikin sojoji jiya Lahadi da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane goma sha hudu. Babu wanda ya dauki alhakin fashe fashen uku da suka auku a garin Bauchi ‘yan sa’oi bayan rantsar da shugaban kasa Goodluck Jonathan a babban birnin tarayya Abuja. Jiya Lahadi ‘yan sanda suka ce mutane goma ne suka rasu sai dai wakilinmu na jihar Bauchi ya aiko rahoto yau cewa adadin mutanen da suka mutu ya haura zuwa goma sha hudu, yayinda a kalla mutane ishirin da biyar suka ji raunuka. Shugaba Goodluck Jonathan yana fuskantar kalubalar hada kan kasar da ke fama da tashen tashen hankula dake da nasaba da siyasa. Sama da mutane dari takwas suka mutu a tashe tashen hankalin da suka biyo bayan sanar da Mr. Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan Afrilu.
Yansanda a arewacin Najeriya suna bincike fashe-fashen boma baman da suka auku a wani barikin sojoji jiya Lahadi da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane goma sha hudu.