Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aiyedatiwa Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ondo


Lucky Aiyedatiwa
Lucky Aiyedatiwa

Hukumar zaben Najeriya ta ayyana Lucky Aiyedatiwa na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ondo.

Bayan watanni ana yakin neman zabe, al’ummar jihar Ondo sun kamala zabe a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba, inda Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaben da kuri’u mafiya rinjaye.

Aiyedatiwa, gwamnan jihar mai ci ya samu kuri’u 366,781 inda ya doke abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Ajayi Agboola, wanda ya samu kuri’u 117,845.

Sanarwar ta zo ne sa'o'i bayan da aka fara tattara sakamakon zaben da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Sakamakon karshe ya nuna cewa jam’iyyar APC ta lashe zaben da kuri’u mafiya rinjaye, inda ta yi nasara a duka kananan hukumomin jihar 18.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG