Shugaba Goodluck Jonathan ya sha alwashin farauto wadanda su ka tayar da bama-baman da suka hallaka mutane 32 a birnin Jos a ranar Jumma’a.
Da ya ke jawabi ga jama’a ranar Asabar, Mr. Jonathan yace gwamnati za ta yi duk abin da ka yiwu don zakulo wadanda suka haddasa kashe-kashen.
Babban Hafsan Sojoji, Laftana-Janar Azbuike Ihijirika ya ce bama-baman da aka tayar a Jos aiki ne na ta’addanci, wanda ya samo asali daga rashin ingantaccen tsarin tara bayanan sirri. Ya ce daga yanzu za a inganta tsarin tara bayanai a ciki da wajen Jos.
Tashe-tashen hankula tsakanin kungiyoyin addinai da na kabilu sun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane a ciki da wajen Jos a ‘yan shekarun nan. Wannan garin dai na yankin tsakiyar Nijeriya ne, inda ‘yan Arewacin Kasar wadanda akasarinsu Musulmi ne kan hadu da ‘yan Kudancin Nijeriya wadanda akasarinsu Kirista ne.
Hukumomi sun ce mutane 32 sun mutu wasu kuma 74 sun sami raunuka a jerin tashe-tashen bama-baman da su ka auku a Jos ranar Jumma’a da yamma. Akasarin wadanda abin ya rutsa da su masu sayayyar karshe ne na bikin kirsimeti.