Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar EFCC Ta Gayyaci Shugabannin Kamfanonin Shell Da Haliburton A Najeriya Kan Zargin Sun Bada Cin Hanci


Hukumar EFCC Ta Gayyaci Shugabannin Kamfanonin Shell Da Haliburton A Najeriya Kan Zargin Sun Bada Cin Hanci
Hukumar EFCC Ta Gayyaci Shugabannin Kamfanonin Shell Da Haliburton A Najeriya Kan Zargin Sun Bada Cin Hanci

Talatan nan ne hukumar ta yaki da masu yi wa tattalin arzikin zakon kasa ta bada sanarwar tana son tattaunawa da shugabannin wadan nan kamfanoni kan zargin bada fiyeda dala milyan 400 ga jami'an Najeriya.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta gayyaci shugabannin kamfanin Shell da Haliburton,domin tattaunawa dasu kan zargin bada cin hanci da rashawa ga jami'an Najeriya. Talata nan ce hukumar EFCC ta bada sanarwar tana son ta yi magana da wakilin kamfanin Shell a Najeriya,kan zargin bada cin hancin dala milyan 240.Haka shi ma takwaransa na kamfanin Haliburton EFCC tana son jin ta bakinsa kan zargin kamfanin ya bada cin hancin dala milyan 180.

Gayyatar ta biyo bayan wani bincke da hukumomin Amurka suka gudanar da ya gano mummunar cin hanci da rashawa a hukumar Custom ta Najeriya.

Hukumomin Amurka sun ci tarar reshen kamfanin Shell dake Najeriya dala milyan 30, saboda samunsa da laifin bai wa jami’an Najeriya cin hanci da jami’an wasu kasashe shida.

Ana zargin wani kamfanin daga kasar Switzeland mai suna Panalpina daya kware wajen jigilar kaya ta da jiragen ruwa da hanu kan wadan nan zarge zarge.

XS
SM
MD
LG