ABIA, NIGERIA - Wannan na zuwa ne a yayin da wa’adi na tsawon kwana 21 da kungiyar Likitoci ta Najeriya reshen Jihar Abia ta bai wa gwamnatin Jihar akan batun na ci gaba da tafiya.
A cewar Dakta Isaiah Abali, shugaban kungiyar Likitoci a jihar,
“Mun samu zantawa da gwamnatin Jihar, kuma bayan mun tattauna da gwamnan, sai ya tura mu zuwa wurin kwamishinan kiwon lafiya da wasu manyan ma’aikatan gwamnati. Da muka kasa cimma matsaya da su, sai muka bukace su, su koma ga gwamna su tambayo basukan wata nawa ne zai biya. Daga bisani gwamna ya ce iya abin da zai biya shi ne basukan wata biyu a wannan Nuwamba da kuma basukan wata biyu a Disamba. Kuma bayan wannan sai a sake wani zama. Amma sam ba mu yarda da hakan ba, kuma har yanzu wa’adin da muka basu na nan.”
A ranar 17 ga wannan watan Nuwamba ne kungiyar Likitocin ta bai wa gwamnatin Jihar Abia wa’adin tsawon mako ukku ta biya Likitoci basusukan albashi na tsawon wata 24 da suke bin ta, ko kuma su tsunduma yajin aiki.
Sai dai wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Mista Mike Ukandu na ganin ba lallai ba ne wannan wa’adin da likitoci suka bada ya yi tasiri.
Ya ce, “Suna iya daukar kowane mataki a matsayin kungiya. Amma na san cewa zai yi matukar wuya su samu biyan bukata. Kawai suna yi ne don su sa gwamnati ta yi abin da ya kamata ta yi.”
Saurari cikakken rahoton daga Alphonsus Okoroigwe: