Dan takarar jam’iyyar hamayya Macky Sall yace za a shiga sabon babi a kasar Senegal, a bayan da ya samu nasara a zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka yi jiya lahadi.
Sakamakon da ba hukuma ce ta fitar da shi ba ya nuna cewa Mr. Sall ya doke shugaba Abdoulaye Wade, wanda yake neman wa’adi na uku da ake cacar-baki kai a kan kujerar shugaban kasa.
Mr. Sall ya fadawa ‘yan jarida yau litinin cewa wannan zabe nasara ce ga dukkan ‘yan kasar Senegal.
Magoya bayansa dai sun yi gangami a Dakar, babban birnin kasar, domin murnar wannan nasara da ya samu.
Shugaba Wade ya fada cikin wata sanarwar da ya bayar a yau litinin cewa ya buga waya ma Mr. Sall yana taya shi murnar nasarar da ya samu. Har ila yau ya godewa magoya bayansa ya kuma yi kira a gare su da su yi shirin zaben majalisar dokokin dake tahowa.
Wannan mika kai da shugaba Wade yayi cikin sauri ya kawar da fargabar cewa shugaban mai shekaru 85 da haihuwa zai yi kokarin makalewa a kan kujerar mulkin kasar.
Har ila yau, wannan sakamakon ya kara karfafa martabar Senegal a idanun duniya a zaman kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya ta lumana a Afirka, inda aka san wasu kasashe da fuskantar juyin mulkin soja, ko zub da jinin siyasa ko kuma irin shugabannin nan da idan sun hau mulki sai su mayarda kujerar ta har tsawon rayuwa.
Yau litinin a titunan Dakar, mutane sun fito domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba, abinda ya kawar da tsoron fitina.
Mr. Sall yana daya daga cikin ‘yan takara 13 na hamayya a zagayen farko na wannan zabe da shugaba Wade ya zamo na daya da kashi 35 cikin 100. Sauran ‘yan takarar da suka sha kaye sun juya goyon bayansu ga Mr. Sall wanda yayi alkwarin sauyin gwamnati da sauko da farashin muhimman kayan abinci.