Da yake bayani ta kafafen gwamnatin Nijar, babban alkali mai kare muradun hukuma a kotun birnin Yamai mai shara’a Maman Tsayabou Issa ya tabbatar da cewa ya zuwa ranar Laraba kimanin mutane 250 ne ke tsare a hannun jami’an ‘yan sanda.
Wannan ya biyo bayan tarzomar da aka fuskanta a birnin Yamai da nufin nuna rashin yarda da sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka yi a ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairu, wanda ake ci gaba da bincike domin gano masu hannu a wannan al’amari.
Shugaban kungiyar Voix des Sans Voix, Nassirou Saidou, ya ce tun da aka fara zaben wannan shekara ‘yan siyasa ba su hada kan su ba wurin tafiya kan su ya rarrabu tsaknin masu mulki da yan adawa.
Saidou ya kuma kara da cewa, wannan abu da ya faru tun farko abu ne da suka tabbatar zai faru, idan kuma ka dubi yadda yanayi gari babu wanda ya ke fitowa hankalin sa kwance.
Tsohon kwamandan rundunar mayakan jamhuriyar Nijar Janaral Moumouni Boureima Tchanga na daga cikin mutanen da ke tsare a yanzu haka, yayin da wata majiya ta ce hukumomi na neman wasu shugabannin ‘yan adawa.
Sai dai shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta CODDAE, Alhaji Moustapha Kadi, ya ce zama kan teburin sulhu ita ce hanya mafi a’ala ga yanayin da Nijar ke ciki a yau.
A can baya, babban alkali mai kare muradun gwamnati ya sanar cewa hukumomi sun zuba ido domin ganin abubuwan da ka iya biyo bayan munanan kalaman da ake zargin wasu ‘yan siyasa da furtawa a lokacin yakin neman zabe.
Tuni kungiyoyin kare hakkin dan adam suka fara kiran bangarorin siyasar kasar da su maida zuciya nesa.
Daya daga cikin Shugabannin matasa, Kabirou Issa, ya ce bai yi mamakin matakin kama wadanan mutane ba.
Koda yake kura ta dan lafa a wasu unguwanin a birnin Yamai, amma yau Alhamis, matasa suka afkawa gidan wakilin Sashen Faransanci na gidan radiyon Faransa Moussa Kaka da ke unguwar Lossa Goungou a bisa zarginsa da goyon bayan jam’iyya PNDS Tarayya mai mulki.
Jiya Laraba kuwa wani jami’in tsaro ya rasa ransa lokacin da wasu masu zanga zanga suka yi yunkurin kutsawa gidan wani dan siyasa a unguwar Koubia.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: