Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Bazoum Mohamed Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa


Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

Yau da maraice hukumar zaben jamhuriyar Nijer ta fitar da kammalallen sakamakon zagaye na 2 na zaben da aka gudanar a ranar 21 ga watan fabrerun 2021.

Alkaluman hukumar sun yi nuni da cewa, dan takarar jam’iya mai mulki Bazoum Mohamed ya doke abokin karawarsa Mahaman Ousman sai dai tuni magoya bayan dan takarar na ‘yan adawa suka yi watsi da wannan sakamako saboda a cewarsu an tafka magudi.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Shugaban hukumar zaben Nijer Me Issaka Sounna ya bayyana cewa, mutane million 4 484572 suka kada kuri’a a zaben na 21 ga watan fabreru, kuma Bazoum Mohamed wanda ya sami kuri’u 2501 459 ya lashe wannan zabe da kashi 55.75 daga cikin 100 yayinda Mahaman Ousman ya sami kuri’u 1985736 wato kashi 45.25 na yawan kuri’un da aka kada.

wa-zai-gaji-shugaba-mahamadou-issoufou

bazoum-mohamed-na-jin-kamshin-kujerar-shugaban-kasar-nijar

wai-ko-wa-ake-ganin-zai-lashe-zaben-shugaban-kasa-a-nijar

zanga zangar da aka gudanar a birnin Yamai na Nijar
zanga zangar da aka gudanar a birnin Yamai na Nijar

Tuni mukarraban dan takarar na jam’iya mulki suka bayyana farin ciki da samun wannan galaba. Alhaji Boubacar Sabo shine sakataren harakokin zaben PNDS Tarayya..

Sai dai ana gab da bayyana wannan sakamako ‘yan adawa suka bukaci hukumar zabe ta dakatar da fitar da sakamakon saboda a cewarsu akwai alamun magudi tattare da alkulaman da ta riga ta fitar..

Fitar da wannan sanarwa ke da wuya, wasu matasa suka fantsama a titunan birnin yamai suna kone kone tare da rera taken jam’iyar RDR Canji, suna masu nuna rashin gamsuwa da wannan sakamako duk kuwa da cewa a lokacin barkewar wannan tarzoma hukumar zaben ba ta kammala aikin tantance alkaluman da suka rage ba.

zanga zangar bayan sanar da sakamakon zabe a nijar
zanga zangar bayan sanar da sakamakon zabe a nijar

An dai dauki lokaci mai tsawo ana ba ta kashi tsakanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma da wadanan matasa.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:

CENI: Bazoum Mohamed Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa: 3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG