Tun bayan kammala zaben shugaban kasar jamhuriyar Nijar zagaye na biyu da aka yi a karshen makon nan, inda 'yan takara biyu da suka samu kuri'u mafi rinjaye a zagayen farko suka sake karawa, hankalin duniya yanzu ya koma kan kasar don samun sakamakon zaben,
Hukumar zaben jamhuriyar ta Nijar, ta sanar da cewar daga cikin da'irori 266 da ake da su a kasar, zuwa yanzy an kammala kidaya kuri'u na da'irori 197, haka na nuna cewar an kidaya fiye da kashi buyi cikin ukku na baki daya da'irorin da ake dasu a kasar baki daya.
Hukumar ta bayyana sakamakon da ke nuna cewar Muhammad Bazum shi ke kan gaba a baki dayan kurin'un da aka kada, sai abokin takarar shi Alh. Muhammad Usman, wanda ke biye da shi.
Ana sa ran samun takamaiman sakamakon da zai nuna wanda ya lashe zaben, nan da zuwa ranar Laraba da yamma. Sai ku cigaba da bibiyar shafukanmu don samun karin bayani akan sakamon zaben.
Ana iya sauraron wannan rahoton cikin sauti, inda Mahmud Lalo ya zanta da wakilin Muryar Amurka, Sule Munmuni Barma.