Bayanan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta OCRTIS ta bayar a dangane da wani lodin miyagun kwayoyi da ya taso daga Mali don ratsa arewcin Nijer da nufin shiga kasar Libya ne suka bada damar cafke magajin garin Fachi da direbansa dauke da kg sama da 200 na hodar iblis.
A washegarin faruwar wannan al’amari hukumomi sun tasa keyar wadanan mutane zuwa birnin Yamai domin ci gaba da bincike kamar yadda aka bayyana a lokacin gabatar da wadannan mutanen ga manema labarai.
Nana Aishatu Usman Bako, mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan birnin, ta ce gwaji ya tabbatar da cewa hodar iblis ce kuma mutune 3 na hannun hukumar yanzu haka wasu kuma sun tsere amma ana nemansu. Aishatu ta kuma bayyana cewa an samu wayoyin hannu 8 da bindigogi 2 da kuma motoci 2 a hannunsu.
A Maradi ma hukumar OCRTIS ta yi nasarar kama wani hamshakin dan kasuwa dake safarar miyagun kwayoyi inda aka tarar da tarin kwalayen wasu kwayoyi dangin Tramadhol da ya boye a wani gida dake unguwar Ali Dan Tsoho.
Wata tawagar mambobin gwamanti da lauyoyin gwamnati a karkashin jagorancin ministan cikin gida Hama Souley, ta ziyarci ofishin OCRITIS domin jinjinawa ma’aikatanta. Suna masu cewa za a dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an gudanar da cikakken binciken da zai bada damar hukunta masu hannu a wannan kazamar sana’a.
Cikin irin wannan yanayi na fuskantar yaduwar fataucin miyagun kwayoyi, kungiyoyi masu zaman kansu na da rawar takawa wajen aiyukan waye kan al’umma a cewar Ganda Saley shugaban kungiyar ADENA mai yaki da fataucin miyagun kwayoyi.
Wannan shine karon farko da ake kama wani ma’aikaci cikin harkar miyagun kwayoyi a Nijer, ko da yake a shekarar 2017 ma jami’an tsaron kasar Gambia sun kama wani mashawarcin shugaban majalisar dokokin Nijer na wancan lokaci dauke da hodar iblis.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: