Kimanin ‘yan Rwanda takwas daga cikin wadanda suka sami mafaka a Nijar ne hukumomin kasar suka bai wa wa’adin mako guda da su gagauta ficewa daga kasar.
Mutanen wadanda aka zayyana sunayensu a wata sanarwar da gwamnatin Nijar ta bayar, na daga cikin wadanda kotun hukunta manyan laifika ta kasar Rwanda TPIR ta samu da hannu a yakin basasar da aka yi fama da shi. Da alama matakin gwamnatin ya sami karbuwa a wajen wasu shugabannin kungiyoyin kare hakkin jama’a.
Sai dai wani dan siyasa mai fafitika ta yanar gizo, "Blog" Bana Ibrahim na ganin rashin dacewar wannan mataki a bisa la’akari da tanade-tanaden wasu mahimman dokokin kasa da kasa.
To amma mahukuntan na Nijer a wannan sanarwa sun bayyana dalilan diflomasia a matsayin hujjar da ta kaisu ga yanke shawarar korar wadanan ‘yan kasar na Rwanda.
‘Yan kabilar Tutsi sama da 800,000 ne aka hallaka a yakin basasar da ya daidaita kasar Rwanda a 1994. Jajircewar kasashen duniya ta taimaka wajen farfado da al’amura a wannan kasa yayinda aka kafa wata kotun musamman TPIR da nufin hukunta masu hannu a wannan tashin hankali inda wasu suka yi amfani da wani gidan rediyon kasar wajen yada sakwannin kyamar al’umar Tutsi a wancan lokaci.
Saurari rahoto cikin cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: