Wakilin UNICEF ya bayyana cewa, tunkarar matsalar aurad da yara mata masu kananan shekaru tamkar gwagwarmaya ce da matsalolin da ke da nasaba da tattalin arziki, da al'adu, da yaki da talauci. A saboda haka 'yan jarida na da rawar da zasu taka a wannan fannin. Ganin yadda suke da karfin fada a ji a cikin al'umma.
Shugaban ma'aikatar da ke kula da inganta rayuwar mata,da bada tallafi ga yara kanana reshen Tahoua Mallam Alhassan Isa, ya kara jaddada muhimmancin wannan lamari idan aka yi la'akkari da yadda yake da nasaba da take hakkin yara kanana kuma auren wurin na aukuwa sosai a jihar Tahoua.
Saurari rohoton
Facebook Forum