Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An ji karar harbe harbe A Dandalin Tahrir Dake Alkahira


Masu zanga zanga suke rera wakokin nuna kyamar gwamnatin Masar a birnin Alexandria.
Masu zanga zanga suke rera wakokin nuna kyamar gwamnatin Masar a birnin Alexandria.

An ji karar bindiga da safiyar Asabar din a dandalin ‘yanci ko Tahrir a birnin Alkahira da shiga yini na 12 da fara zanga zanga cikin kasar.

An ji karar bindiga da safiyar Asabar din a dandalin ‘yanci ko Tahrir a birnin Alkahira da shiga yini na 12 da fara zanga zanga cikin kasar.

Babu rahotanni nan da nan, ko akwai wadanda harbe harben ya rutsa dasu, a yayinda dubban jama’a suke ci gaba da zama cikin dandalin.

Ranar jumma’a dubun dubatan masu zanga- zangar kyamar gwmnati suka cika dandalin,wasu suna rera wakoki wasu suna kada tutar kasar mai launin ja,da fari da baki.Wasu suka girke manyan kellaye,akalla mutum guda ya makala mutum mutumin shugaba Hosni Mubarak.

A jiya jumma’an masu zanga-zanga sun ayyanata a matsayin ranar da zasu yi odabo da Mr. Mubarak,kodashike shugaban cikin jawabin da ya yi cikin makon nan ya yi alwashin zai kammala wa’adin mulkinsa.

Haka kuma a jiya jumma’an Frayin Ministan Ahmed Shafiq, ya yi alkawarin gwamnati ba zata dauki wani mataki kan masu zanga- zanga dake dandalin Tahrir ba.

Haka kuma gwamnatin ta dan sassauta dokar hana yawon dare da aka kafa na mako daya zuwa yanzu.Yanzu dokar zata fara aiki daga karfe bakwai na yamma zuwa shida na safe,maimakon karfe biyar na yamma zuwa bakwai na safe,kodashkie masu zanga- zanga basa mutunta dokar.

A yinin jiyan,babban jakadan kungiyar larabawa Amr Mousa, ya ziyarci masu zanga zanga a dandalin na Tahrir,yana daya daga cikin fitattun ‘yan siyasar Masar, ya riki mukamin ministan harkokin wajen Kasar. Tashar radiyon Faransa da ake kira Europe 1,ta ambaceshi yana cewa zai yi shawarar ko ya yi takarar shugaban kasa,amma ya hakikance cewa shugaba Hosni Mubarak zai kammala wa’adinsa.

An sami rahotannin an gwabza fada,da kuma jin harbe harbe bindiga a iska,yayinda wasu magoya bayan shugaba Mubarak suka yi kokarin shiga dandalin Tahrir.

Rundunar sojojin kasar suka hana su shiga,daga bisani suka hallara a wani bangaren birnin Alkahira suna kiran yinin na jiya, “ranar nuna biyayya”.

Haka kuma dubban masu zanga zanga dake kyamar gwamnati sun yi gangami a birnin Alexandria inda suka yi jerin gwano cikin lumana.Wakilin Muriyar Amurka yace masu kyamar gwamantin Mubarak sunyi zanga zanga a tsakiyar birnin, wasu kuma a Masallaci.

Rahotanni daga kafofin yada labarai sun ce an yi irin wadan zanga zanga a Suez, Isami’ila, da ma wasu biranen kasar.

XS
SM
MD
LG