Mataimakin Shugaban Kasar Misra, Omar Suleiman ya yi watsi da kiraye-kirayen Shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus nan da nan, ya ce wannan hanzarin zai haifar da rudami. Wannan jawabin nasa ya zo ne a daidai lokacin da masu zanga-zanga da jefe-jefen duwatsu su ka bijire wa dokar yana yawo a babban birnin kasar, al-Khahira, inda aka yi ta jin karar harbe-harben bindigogi a bisa tituna har zuwa dare. Masu zanga-zangar kin amincewa Mr Mubarak ya cigaba da zama bisa karagar mulki har sai karshen wa’adinsa, sun sha alwashin kaddamar da wata gagarumar zanga-zanga a gobe Jumma’a a yinkurinsu na matsa wa shugaban lamaba ya sauka. Saidai, Mr. Suleiman ya baiyana arangamar da aka yi tsakanin magoya baya da wadanda basu goyon bayan shugaba Mubarak a zaman makarkashiya. Yace babu hannun gwamnati amma za’a gano wadanda suka kitsa wannan makarkashiya.
Mataimakin kasar Masar ya ce Saukar Mubarak daga karagar mulki zai janyo rudami

Mataimakin Shugaban Kasar Misra, Omar Suleiman ya yi watsi da kiraye-kirayen Shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus nan da nan