Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin shugaban kasar Masar ya gana da kungiyar Muslim Brotherhood


Mataimakin shugaban kasar Masar Omar Suleiman.
Mataimakin shugaban kasar Masar Omar Suleiman.

Mataimakin shugaban kasar Masar ya fara tattaunawa da babar kungiyar hamayyar kasar Muslim Brotherhood, da sauran kungiyoyin hamayya da zumar warware zanga zangar kin jinin gwamnati

Mataimakin shugaban kasar Masar ya fara tattaunawa da babar kungiyar hamayyar kasar Muslim Brotherhood, da sauran kungiyoyin hamayya da zumar warware zanga zangar kin jinin gwamnatin da aka kusa shafe makonni biyu ana gudanarwa. Mataimakin shugaban kasa Omar Suleiman ya gana yau lahadi da wakilan kungiyar Muslim Brotherhood, da shugabannin jam’iyun da basu sa addini a harkokin siyasa, da kuma ‘yan siyasa masu zaman kansu. Shugaban kungiyar Muslim Brotherhood Mohammed Mursi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, kungiyar tana kan bakanta a bukatar ganin kawo karshen mulkin shekaru 30 na shugaba Hosni Mubarak. Wannan tattaunawar ita ce ta farko cikin shekaru da dama tsakanin gwamnatin kasar Masar da kungiyar Brotherhood, wadda aka haramta, kungiyar dake samar da ababan jin dadin rayuwa ga talakawan kasar wadda kuma take da membobi a majalisa a matsayin ‘yan indifenda.

XS
SM
MD
LG