'Yan sanda a kasar Mozambique su na zaune cikin damarar fuskantar karin zanga-zanga ta nuna rashin yarda da karin farashin kayan abinci da aka yi.
An kashe mutane 10, yayin da wasu fiye da 400 suka ji rauni a kwanaki ukun da aka shafe ana zanga-zanga a makon da ya shige.
'Yan sanda sun ce ana ta aikewa da sakonnin "text" ta wayoyin salula daga wasun da ba a san ko su wanene ba, inda ake kira ga mutane da su sake fitowa zanga-zanga a ranar litinin.
Komai tsit lahadi a Maputo, babban birnin kasar, amma 'yan sanda sun ce su na yin sintiri a titunan birnin domin hana sake abkuwar wannan tashin hankali.
An fara wannan zanga-zanga ranar laraba a Maputo, a bayan da gwamnati ta bayar da sanarwar karin farashin buredi, da ruwa da kuma wutar lantarki.
A wasu wuraren, masu zanga-zanga sun cinna wuta a tayu, suka tare hanyoyi da su, abinda ya kai su ga yin arangama da 'yan sanda.
Gwamnati ta ce hauhawar farashi a fadin duniya ta sanya ta yi karin farashinw adannan abubuwa, kuma ba zata rage su ba.