Dakarun kasar sun yiwa helkwtar lardin Anbar din kusan zobe, domin sun danna zuwa kan Birnin. Yanzu saura kilomita 15 su shiga Ramadi, bayan da suka shafe lokaci mai tsawo suna fafatawa saboda tsananin zafi, da azumin watan Ramadan, da kuma aikin Hajji.
Kakakin rundunar taron dangi da Amurka take yiwa jagoranci da take fafatawa da 'yan binidgar kanal Steve Warren ya gayawa manema alabarai haka jiya Talata ta bidiyo kai tsaye daga Bagadaza.
Wannan kiran da kuma dannawar da dakarun suke yi yana zuwa ne a dai dai lokacinda rundunar taron dangin ta zafafa kai hare hare da jiragen yaki a ciki da kewayen Ramadi cikin kwanaki 10 da suka wuce. Amurkan tace ta kai hare hare har sau 52 a yankin.
Sojojin Iraqi sun kewaye birnin Ramadi, sun kama duka kofofi huduna shiga birnin.Kanal Warren yace yanzu abunda ya rage musu shine shiga sannu ahankali cikin wurare da suke da cunkuson jama'a.