Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane Talatin ne Suka Hallaka a Kasar Iraqi


Baraguzen motar da aka yi kunar bakin wake da ita
Baraguzen motar da aka yi kunar bakin wake da ita

Hare-haren da aka kai a kasar Iraqi ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla talatin da kuma raunata wasu.

A can kasar Iraq kuma, hare hare dabam dabam da aka kai a kasar sun kashe akalla mutane talatin da uku da raunana wasu da dama.

Hari mafi muni a jiya Litinin ya faru ne a Suwayrah kudu da birnin Bagadaza, lokacinda wani mai harin kunar bakin wake ya apkawa wurin bincike na yan sanda da motarsa dake dankare da nakiyoyi ya kashe akalla mutane goma da raunana mutane goma sha bakwai.

A garin Madain dake kusa kuma, wani mai harin kunar baki wake cikin mota ne ya apkawa wurin binciken sojoji, ya kashe sojoji biyu da ranana biyar.

Haka kuma wani bam da aka boye a gefen hanya ya kashe wani sojan Iraq da raunana mutum uku a birnin Mishahda dake arewacin kasar. A Latifiyah kuma kimamin kilomita talatin, kudu da birnin Bagadaza, wasu yan bindiga da suke gudun masifa cikin mota suna harbi ne, suka kashe mutum daya da raunana mutum biyu.

Hare haren bama bamai guda hudu da aka kai a unguwanin birnin Bagadaza jiya litinin da maraice kuma sun kashe mutane goma sha hudu da raunana mutum arba'in.
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG