Hare haren bama bamai da aka boye cikin motoci sun kashe mutanen da yawansu ya kai talatin da bakwai a Iraq a jiya Alhamis. Ana kyautata zaton kila an auna kai hare haren ne akan 'Yan Shiya da Kurdawa.
Tashin bam na farko ya faru ne a shagon shan shayi a wata unguwar Kurdawa a birnin Kirkuk. Sa'anan kuma tashin bam na biyu ya faru ne a yankin birnin Sadr na birnin Bagadaza.
Kusan kullu yaumin ake kai hare haren ta'adanci a birnin Bagadaza da wasu biranen kasar Iraqi.
Kungiyar Islamic State ko IS a takaice tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai yawancin hare haren
A halin da ake ciki kuma, sabon jakadan Amirka a Iraqi, Stuart Jones yace sojojin Amirka suna da kariyar da ba za'a hukunta su a Iraqi ba.
Jakadan Jones ya shedawa kamfanin dilancin labarun Associated Press cewa ya samu wannan tabbaci daga Prime Ministan Iraq Haider Al-Abadi. Yace kariyar wani bangare ne, na jadawalin dabarar da aka shata tsakanin Amirka da Iraqi, daya tanadi sojojin Amirka zasu taimaka wajen baiwa sojojin Iraqi horo da kuma taimakon kayan aiki a kokarin da suke yi na murkushe yan yakin sa kan kungiyar IS.