Taron, wanda shine irin shi na farko a Kudancin Kaduna, zai kwashe kwanaki uku ne ya na nemo mafita game da hauhawar hare-hare da rikice-rikice a kudancin jihar Kaduna
Hukumar kula da ziyarar birni Mai Tsarki na Kirista a Najeriya zuwa Jerusalem da wasu makusantan gwamnati ne suka shirya wannnan taron da aka fara a jiya Talata, kuma shugaban hukumar Rev. Yakubu Pam wanda shine shugaban kungiyar Kiristocin Arewacin Najeriya ya bayyana tasirin taron.
Ya ce “zasu tabbatar an kiyaye sharudan da taron zai ajiye wurin samar da zaman lafiya da kuma kawo karshen tashin hankali da ake samu a yankin”.
Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban darikar Fentacostal na Kasa Apostle Emanuel Nuhu Kure ya kuma yi kira ga duk wanda ke da wata hikimar da zai taimakawa kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a kudancin Kaduna, ya bada gudunmuwar sa.
Shugaban kungiyar Fulani ta Miyatti Allah a jahar Kaduna, Alh. Haruna Usman Tugga ya ce taron ya dace sai dai ya bayyana rashin jin dadin ganin wadansu al'umma ba su halarci taron ba. Ya kuma gargadi jama’a da su daina daukar doka da hannun su, kana su sanar da hukuma a duk lokacin da aka samu barkewar rikici.
A nashi bayanin, Pastor James Wuye shugaban kwamitin tsare-tsare na wannan taro, ya ce wannan taro zai tabbatar da an kawo karshen rikice-rikice da kuma kulla kyakkyawar ma’amala tsakanin jama’a.
Tuni dai hauhawar hare-hare a kudanciin Kaduna ya jawo kungiyoyi daban-daban don lalubo mafita game da matsalar tsaro a yankin baki daya kamar yadda ko a kwanakin baya gamayyar kungiyoyn matasa na Arewachin Najeriya su ka shirya makamanchin wannan taro.
Ga rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:
Facebook Forum