Tun ranar Asabar da ta gabata ne rahotanni suka mamaye kafafen yada labarai na yanar gizo a kan yadda ‘yan ta’addar boko haram ke shirin kawo farmaki zuwa birnin tarayya, Abuja wadda aka danganta fitar da sanarwar da hukumar kwastam, sai dai hadimin hulda da jama’arta ya nesanta hukumar da fadin abin da ake ta yadawa a kafafen yanar gizo sannan ya yi karin haske a kan lamarin, ya na mai cewa babu ruwan hukumar da yaduwar labarin.
Rahotannin dai sun bayyana cewa ‘yan ta’adar sun kafa sansanoni a dajin Kunyen dake kan hanyar filin tashi da saukar jiragen saman Nnamdi Azikiwe kusa da rukunin gidajen sashin tattara bayanan sirri na rundunar sojin kasar a birnin Abuja, dajin Robochi a Gwagwalada, dajin Kwaku a Kuje, dajin Umaisha dake karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa, sai kuma dajin Gegu dake kusa da garin Idu na jihar Kogi.
Da muka tuntubi babban daraktan hukumar wayar da kan yan Najeriya ta NOA, Dr. Garba Abari a kan sanarwar da ake dangantawa da hukumar kwastam, ya ce abin yi kawai shi ne bayar da hadin kai ga jami'an tsaro.
A wani bangare kuwa, kwamishinan ‘yan sanda da ke kula da babban birnin tarayya Abuja, Bala Ciroma, ya yi bayani a kan matakan da ake dauka kan wannan lamari.
Shalkwatar rundunar sojojin Najeriya ta bakin daraktan yada labarai, John Enenche, ta kara jaddada wa mazauna birnin Abuja da jihohi makwabta cewa hukumomin tsaron kasar na cikin shirin ko-ta-kwana domin yaki da miyagun iri a kowane lokaci ta hanyar yin sintiri ba dare ba rana domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mazaunan Abuja da kewaye.
Saurara cikakken rahoton daga Halima AbdurRa'uf:
Facebook Forum