Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Gudanar Da Taron Kungiyar Yada Labaran Afurka Karo na 14 A Abuja


Bannerfor the 14th General Assembly of the AUB in Abuja, Nigeria
Bannerfor the 14th General Assembly of the AUB in Abuja, Nigeria

An samu mahalarta taron daga kasashen duniya daban daban ciki har da Amurka. Taron zai duba abubuwa da dama kama daga gudunmawar da kafafen yada labarai su ke bayarwa wajen inganta cinakayya da kalubalen yada shirye shirye a yanayi na na'ura mai aiki da kwakwalwa da kuma dijital ko lataroni.

Taken taron na bana shi ne "Tasiri da kalubalen yada labarun Afruka a cikin sauyin dijital na duniya". Taro ne da gamayyar Kungiyoyin yada labarai a Afirka ta shirya tare da hadin gwiwar Hukumar telebijin ta Najeriya wato NTA.

Wanan taro zai bada dama a fahimci halayen kafofin yada labaru na Afirka ta manyan batutuwan dijital da ke canja duniya. Hakan zai bai wa 'yan kasuwa, manyan manajoji, malamai da masana damar yin aiki kan samar da arziki a bangaren yada labarai.
A jawabinsa, Salihu Abdulhamid Dembos, shugaban Hukumar telebijin ta kasa a Najeriya NTA, ya yi bayani cewa kowace shekara ana gudanar da irin wannan taron wanda yake hada kan shugabannin gidajen yada labarai na telebijin da radiyo daga dukkannin sassan kasashen Afirka, inda sukan yi bitar kalubaloli da nasarorin da nahiyar Afirka ta ke samu ta fannonin yada labarai.
VOA Africa Division Director Salwa Jaafari
VOA Africa Division Director Salwa Jaafari
Abdulhamid ya kara da cewa, an samu koma baya a nahiyar Afirka ta fannin kirkira, kuma saboda haka ne aka gayyato baki daga kasashen waje irin su nahiyar Turai, da Amurka, da kasar Rasha inda za su tattauna hanyoyin samun nasarori masu muhimmanci a nahiyar.
A nasa bangaren kuma, shugaban Hukumar da ke kula da kafafen yada labarai ta kasar Najeriya Balarabe Shehu Ilella, ya yi nazarin taron inda ya ce yana da muhimmanci sosai domin za a yi kokarin canja yadda wasu kasashe suke kallon Afirka, domin a yanzu taron ya nuna cewa an kara samun zaman lafiya da hadin kai a Nahiyar Afirka sabanin yadda ake kallon nahiyar.
Balarabe ya ce nahiyar tana da kalubalen kayan aiki na zamani, saboda haka za a yi musayar ra'ayi wajen samun sabbin hanyoyin amfani da basirar kasashen da suka cigaba.
Daya cikin manyan bakin da suka halarci taron kuma babbar darekta mai kula da sashin Afirka na Muryar Amurka Malama Salwa Jaafari ta bayyana farin cikin kasancewarta a wannan taron kuma ta ji dadin gayyatar ta da aka yi. Salwa ta ce wannan wata dama ce da za ta hadu da mutane daban daban da suke da manufa iri daya kuma masu wakilcin kafafen yada labaru daban daban daga kasashen duniya. Salwa ta ce ta hadu da mutanen da za ta iya hulda da su wajen yada shirye shiryen Muryar Amurka. Salwa ta ce abu na farko shi ne tattauna yadda ayyukan kafafen yada labaru ke komawa na zamani. Ta ce wannan abu ne da zai zama mata abin alfahari da kuma jin dadi ganin yadda ta samu karbuwa wajen abokan aiki a Najeriya da na kasashen Afirka baki daya
Salwa Jaafari, Africa Division Director of the Voice of America
Salwa Jaafari, Africa Division Director of the Voice of America
Za a cigaba da taron har ma za a shirya wani gagarumin baje kolin masu fasaha daban daban daga sassa daban daban na nahiyar a bainar baki na musamman.
A saurari rahoton Medina Dauda:
SALWA JAFARI AT AUB IN NIGERIA.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
XS
SM
MD
LG