Tun cikin makon jiya wasu lauyoyi masana harakokin zabe suka shawarci madugun kyampen na Hilary Clinton, watau John Podesta da cewa ya sa a je a sake kirga kuri’un da aka jefa a jihohin Wisconsin, Pennsylvania da Michigan saboda suna jin an aibanta komputocin da aka yi anfani da su wajen jefa kuri’un, kamar yadda mujallar “New York” ta nuna.
Lauyoyin sun lura da cewa kuri’un goyon bayan HC sun kasa da maki 7 a yankunan da aka yi anfani da komputa wajen jefa kuri’u, ba kamar goyon bayan da ta samu a yankunan da aka yi anfani da kuri’un takarda ba.
Lauyoyin sunce karin hujjarsu na neman a sake kirga kuri’un shine saboda yawan kurik’un da Donald Trump ya samu a duk wadanan jihohin ukku basu shige 2% na dukkan kuri’un da aka jefa a jihohin ba.