Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsarin Electoral College Ya Sa Trump Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Amurka


Shugaban Amurka Mai Jiran Gado, Donald Trump
Shugaban Amurka Mai Jiran Gado, Donald Trump

A zaben shugaban Amurka da aka gudanar kawo yanzu kidgdiga na nuni da cewar Hillary Clinton ta wuce shugaban kasa mai jiran gado Donald Trump da ya ci zaben zuwa fadar White House da kuri’u miliyan biyu. Amma shi yayi nasara ne saboda ya samu kuri’un Electoral College masu yawa fiye da Hillary Clinton abun da ya sa ya zama shugaban kasa na 45.

Yayinda ake cigaba da kirga kuri’u a wasu jihohi, bisa ga lissafin jiya Laraba Hillary Clinton nada kuri’u 2,017,563 fiye da Trump kuma zasu cigaba da karuwa saboda akwai kuri’un da har yanzu ba’a kidayasu ba a wasu jihohin da ta ci, musamman jihar California, jihar da ta fi kowace jiha girma da take yankin Pacific.

Ko menene ma ya faru, ko ta yaya kuri’unta suka karu, kuri’un da Clinton ta samu ba zasu canza sakamakon zaben da aka yi ranar 8 ga wannan watan Nuwamba ba. Zata zama ‘yar takara ta biyar a tarihin Amurka, kuma ta biyu cikin shekaru 16 da suka gabata da ta fi samun kuri’u amma kuma ta kasa cin zaben saboda Electoral College da aka kafa shekaru dari biyu yanzu. Kundun tsarin mulkin kasar ya dorawa Electoral College ikon zaban shugabannin kasar.

Zaben shugaban kasa a Amurka ya rataya ne akan kowace jiha da gundumar Kwalumbiya, wato Washington babban Birnin kasar. Duk wanda yaci kowace jiha zai samu kuri’un Electoral College na wannan jihar. Misali,idan jiha nada kuri’n Electoral Cllege 10 kawai komi girmanta, dan takarar da ya lashe zabe a jihar ya samu Electoral College goma ke nan. Babu kari babu ragi. Saboda haka kafin a ce mutum ya ci zaben shugaban kasa to dole sai ya samu kuri’un Electoral College 270 cikin jimillar 538. Jihar da ta fi girma ita ce take da kuri’un Ellectoral College ma fi yawa.

Trump ya ci jihohi da dama da ‘yar rata yayinda Clinton, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka wadda ta kyautata zaton zata zama shugabar kasa mace ta farko ta lashe kuri’un manyan jihohin California da New York. Nasara a wadannan jihohin ta sa ta fi Donald Trump kuri’u amma kuma zai karkare da kuri’un Electoral College 306 yayinda da ita kuma zata tashi da kuri’u 232 bayan da aka kammala kiyadayar duk kuri’un.

Trump hamshakin attajiri wanda biloniya ne yanzu yana fama da nada mukarrabansa da zasu yi aiki dashi a sabuwar gwamnatinsa. Ya taba yin tur da yin anfani da Electoral College wajen zaban shugabannin kasar sai dai kuma yace wata dabara ce dake da mahimmanci domin ta ba kananan jihohi damar yin tasiri a zaben shugaban kasa.

Ranar Talatan nan ya gayawa manema labaran jaridar New York Times cewa shi ya fi son yayi anfani da kuri’un jama’a kawai. Yace shi bai taba son Electoral College ba kafin yanzu saboda ta yin anfani da hanyar ce ya zama Shugaban Kasa Mai Jiran Gado

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG