Wata rundunar 'Yansanda a jahar California ta ce miji da mata da suka harbe suka kashe mutane 14 a wata liyafar karshen shekara ranar Laraba, suna da bama bamai hadin gida, da kayan sarrafasu, da kuma dubban albarusai a dakinsu.
Makasan, Syed Rizwan Farook da matarsa Tashfee Malik sun mutu a musayar wuta da suka yi da 'Yansanda a wani bangare mai gidajen kwana ba nisa daga cibiyar horasda nakasassu, inda suka harbe suka kashe mutane 14, suka raunata 21, a birnin San Bernadino mai tazarar kilomita 100 gabas da birnin Los Angeles.
Baturen 'Yansanda na birnin Jarrod Burguan yace mutanen biyu sunyi harbi sau 75, sannan suka bar irin motocin wasan yaran nan wacce suka nada bama-bamai hadin gida uku, amma suka kasa tashi.
Babbar tambayar anan itace menene dalilinsu na aikata wannan danyen aiki? Shi dai na mijin Syed Farook an haifeshi ne a birnin Chicago anan Amurka, kuma sfeto ne a fannin kiwon lafiya na gwamnati. Matarsa kuma ta shigo nan Amurka neda vizar shirin aure. Babu daya daga cikinsun da aka taba kamawa da aikata wani laifi, kuma basa cikin jerin mutanen da gwamnati take sa ido akansu.