Janar Michael Flynn mai murabus ya yi Allah wadai da wannan gwaji na makami mai linzami, ya na mai bayyanawa da na baya-bayan nan a jerin al'amaru masu nasaba da barazanar Iran ga Amurka da kawayenta cikin watanni 6 da su ka gabata.
Ya ce Shugabannin Iran da ke Tehran sun sami karfin gwuiwar daukar wannan matakin a yanzu ne saboda yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma mai rauni da kuma mai rashin tasiri ce, saboda sauran kasashen da aka yi yarjajejeniyar da su sun kasa daukar matakin taka burki ma Iran game da burinta na soji.
Yayin da yake bayani a Fadar Shugaban Amurka ta White House, Flynn ya zargi tsohon Shugaba Barack Obama da wasu jami'an gwamnatinsa da yin sako-sako da batun Iran.
Da yammacin jiya Laraba, wasu manyan jami'an Fadar White House, sun ce gwajin makami mai linzamin da Iran ta yi da kuma goyon bayan da take baiwa 'yan tawayen Houthi a Yemen masu harzukarwa ne; kuma su na da hadari ga yankin.