Ma'aikatar Harkokin Wajen ta tabbatarwa Muryar Amurka cewa ta karbi wannan takarda. Sai dai jami'an ma'aikatar sun ki su bayyana adadin ma'aikatan da suka sanya hanu mukamansu. Amma wasu majiyoyi sun gayawa Muryar Amurka cewa yawansu ya kai kusan dubu daya.
Idan wannan adadi ya tabbata, zai kasance "abunda ba'a taba ganin irinsa ba" wanda ya ninka har sau 20 yawan wadanda suka sanya hanu kan irin wannan takaradar koke gameda manufar Amurka kan yaki da ake yi a Syria a karkashin gwamnatin Obama, kamar yadda tsohon jakadan Amurka a Syria Robert Ford ya lura.
Tseguntawa duniya batun wasikar da kuma yawan wadannda suka sanya hanu a kai, inji tsohuwar jami'ar difilomasiyya Laura Kennedy, alamu ne da suke nuna irin damuwa kan wannan mataki da illar da zai janyo, kuma ba zai yi katabus ba wajen kare Amurka.
Amma kakakin Fadar shugaban na Amurk Sean Spicer, ya fada ranar Litinin cewa "ma'aikatan na ma'aikatar Harkokin Wajen su mutunta matakin na shugaan Amurka ko kuma su ajiye aikinsu.
Tsoffin jakadu sunyi tur da wannan furuci wanda suka fassara shi a zaman barazana ga ma'aikatan difilomasiyya.