A yau Laraba Firai ministan kasar Australia, Malcolm Turnbull, ya ce Amurka ta himmatu wajen cika alkawarin da ta yi, na sauyawa 'yan gudun hijira dake tsibirin yankin Pacific mazauni, duk da cewar shugaban kasa Donald Trump ya ba da umurnin dakatar da karbar 'Yan gudun hijira na wucin gadi.
Amurkan ta yi wannan alkwari ne a lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka Barack Obama, wanda ya hada da 'Yan gudun hijira kusan 1,200 da aka tsare suna kokarin shiga Australia kuma aka kai su wasu matsugunai a Papua New Guinea da kuma Nauru.
Kakakin Fadar White House Sean Spicer ya fadawa manema labarai a jiya Talata cewa, za a tsaurara bincike akan wadannan 'yan gudun hijra.
Trump ya fara amfani da wannan batu ne a lokacin yakin neman zabe, kan cewa akwai matsala akan wa za a bari ya shiga Amurka.
Da fari dai ya ce zai haramtawa dukkanin Musulmai shiga kasar amma daga baya ya sauya dokar ta sa zuwa bincike mai tsanani.
Mafi yawan 'Yan gudun hijirar da yarjejeniyar ta shafa da Australia 'yan kasar Afghanistan ne da Iraqi da kuma Iran.