Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya caccaki kwamitin sulhu na MDD a kan gazawarta na aiwatar da alhakin da ya rataya a wuyanta wurin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa.
“Kwamitin ya yi watsi da bukatar kara lokacin haramcin makaman na shekaru 13 a kan Iran, lamarin da ya bada dama ga babbar mai bada taimako ga ayyukan ta’addanci ta sayi kuma ta sayar da makamai ba tare da wani takamaiman matakan hani na MDD ba, karon a cikin sama da shekaru goma, Pompeo yana fada a wata sanarwa. “Gazawar kwamitin sulhun na daukar matakin da ya dace a kan tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa wani abu da ba za a lamunta da shi ba.
Kudurin dora haramcin ya samu kuru’u biyu kadai ne, daga Amurka da Jamhuriyar Dominican. Rasha da China sun kada kuri’ar kin amincewa ga matakin haramcin, kana wasu kasashe 11 na kwamitin suka janye daga batun. Kudurin na bukatar akalla kuru’u tara na masu ra’ayi, kuma ba a samu kuru’un da za a tabbatar da kudurin ba.
Ofishin jakadancin China a MDD, ya fitar da sakon twitter cewa sakamakon zaben ya sake nuna matsaya na bai daya na rashin amincewa da kudurin kuma zalunci bai yi nasara ba. Duk wani yunkurin fifita bukatun wani a kan sauran kasashen duniya ba zai yi tasiri ba.
Facebook Forum