Daukan wannan matakin ya biyo bayan gano wasu mutum hudu da ke dauke da cutar a Auckland, birni mafi girma a kasar ta New Zealand da ke kudancin yankin Pacific.
Wadannan mutane sune na farko da aka gano sun harbu da cutar a tsakanin al’uma cikin sama da kwana 100 da ba a ga bullar cutar ba.
A watan Yuni, kasar ta New Zealand ta ayyana samun nasarar dakile yaduwar cutar ta COVID-19.
Hakan ya sa aka dage matakan da aka gindaya, aka maido da harkokin yau da kullam kamar yadda suke gabanin bullar annobar, ko da yake, kan iyakokin kasar sun ci gaba da zama a kulle.
Sai dai cutar ba ta gushe ba, domin bayan an kwashe sama da wata uku ba a samu wanda ya harbu da cutar ba, an samu mutum hudu da suka harbu a tsakanin wasu ‘yan gida daya a birnin na Auckland.
Bayanai sun kuma yi nuni da cewa babu ko daya daga cikinsu da ya yi tafiya zuwa kasar waje, lamarin da ya sa hukumomin kasar suka bazama neman yadda cutar ta sake bulla.
Facebook Forum